Jam’iyyar PDP ta yi nasarar lashe daya daga cikin sakamakon farko da jami’an hukumar zabe ta kasa (INEC) suka bayyana a jihar Osun, yau Asabar.
A rumfar zabe ta 05, mazaba 07 a karamar hukumar Ilesa ta yamma, Sanata Ademola Adeleke na jam’iyyar PDP ya samu kuri’u 47 yayin da Gwamna mai ci Gboyega Oyetola na jam’iyyar APC ya samu kuri’u 17.
Kimanin masu kada kuri’a 120 ne suka yi rajista a rumfar zabe yayin da 71 aka amince da su a ranar zaben.
Jimillar kuri’u 67 da suka samu nasara a yayin da kuri’u hudu suka lalace.