Tawagar sarakunan kabilar Igbo a karkashin kungiyar Ohanaeze Ndigbo Worldwide ta kai ziyarar tuntubar a yankin Arewacin Kasar nan, a wani yunkuri na neman goyon bayan takarar ministan sufuri, Rotimi Amaechi, gabanin zaben shugaban kasa na 2023.
Babban sakataren kungiyar, Mazi Okechukwu Isiguzoro, wanda ya jagoranci sauran shuwagabannin kungiyar a wata ziyarar neman shawarwari ga shugabannin kungiyar matasan Arewa (AYCF) jiya a Kaduna, ya bayyana cewa an ware naira biliyan 10 domin tallafawa dan takarar dan kabilar Igbo.
Ya ce tawagar ta gana da wasu shugabannin addini da na gargajiya na Arewa kan aikin shugaban kasa tare da ba da tabbacin cewa tawagar ‘yan kabilar Igbo a zaben shugaban kasa a 2023 za su ci gaba da zage-zage a duk sassan kasar nan domin sauya mulki zuwa shiyyar Kudu maso Gabas.
Da yake mayar da martani, shugaban kungiyar AYCF na kasa, Alhaji Yerima Shettima, ya ce Arewa ta girma, kuma lokaci ne da ake amfani da batanci, tsoratarwa da tsangwama wajen yin maganganun siyasa ko mulki.
Ya ce: “Siyasa ita ce tattaunawa, ita ce haduwa da jama’a, ba a tattauna a yi ta zage-zage ba, kawai ku zauna a ’yar karamar unguwarku ku yi surutu, toh bashi bane siyasa, wasun mu muna nan ba mu san abin da za a yi ba.
“Ya rage wa ’yan uwan Ibo su tashi tsaye su duba abubuwan da suka wuce gona da iri, su gyara domin ci gaban ku.” Inji shi.