Zabtarewar Bango ta Danne wani mutum a Jigawa
Wani matashi mai shekara 28 mai suna Umar Sale ya mutu sakamakon faɗowar bango a karamar hukumar Taura ta jihar Jigawa.
Kakakin hukumar NSCDC, CSC Adamu Shehu, ya tabbatar wa DAILY POST faruwar lamarin.
KARANTA WANNAN LABARIN: 2023: Zaiyi Wahalar gaske a samu wanda zai Lashe Zaɓen Shugaban Ƙasa a Zagayen Farko – Hunkuyi
Ya ce lamarin ya faru ne a ranar Talata a garin Majia da ke karamar hukumar Taura da misalin karfe 2 na dare.
Shehu ya ce marigayin mai ‘ya’ya uku ne yana tono yashi daga rami don gyara masa gidan laka da ruwan sama ya lalata a lokacin da yashin da ke samansa ya zame ya binne shi da rai.
A cewarsa manoman da ke kewayen yankin sun ji kukan wanda abin ya shafa na neman agaji inda suka garzaya domin ceto shi kuma likitocin sun tabbatar da mutuwarsa.
An sako gawarsa ga iyalansa domin yi masa jana’iza.
A wani labarin kuma: Direba ya saci motar Uwargidansa, ƴan awanni bayan ya fara aiki
A ranar Laraba ne wata kotun majistare da ke Ikeja ta tsare Samuel Harrison a gidan yari na Kirikiri bisa zargin satar motar Ubangidansa da wasu kayayyaki masu daraja.
Alkaliyar kotun, Misis O. O Fajana ta bayar da umarnin tsare wanda ake kara bayan ya amsa laifin hada baki da sata.
Fajana ta dage sauraron karar zuwa ranar 28 ga watan Satumba domin yanke hukunci, kamar yadda NAN ta ruwaito.
Mutumin mai shekaru 46 da haihuwa yana zaune ne a unguwar Ilaje da ke Ajah a Legas.