Yayin da zabukan shekarar 2023 ke kara karatowa, hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, ta ce za a samu ci gaba wajen gudanar da zaben.
Daily Post ta ruwaito cewa, Kwamishiniyar INEC ta kasa mai kula da sa ido da tsare-tsare (PMSC), Farfesa Rhoda Gumus ce ta bayyana hakan, yayin wani taron bita na yini biyu kan Cibiyar Sa ido da Tallafawa Zabe (EMSC) ga shugabannin Sassan Hukumar (HODs) a jiya a jihar Gombe.
KARANTA WANNNA LABARIN: Gwamnatin Kwara Ta Gargadi Shugabannin Makarantun Jihar Kan Karbar Kudade Ba Bisa Ka’ida Ba
Gumus ya ba da tabbacin cewa zabukan 2023 za su kasance cikin walwala, sahihanci kuma za su yi daidai da tsammanin ‘yan Najeriya.
“Zaben 2023 zai kasance mafi inganci, adalci kuma zai kasance cikakke, muna tabbatar wa ‘yan Najeriya,” in ji ta.
Ta kuma ce dukkan matakan da suka dace na gudanar da zabuka na gaskiya da adalci a 2023 hukumar zabe ce ta sanya su, inda ta cigaba da cewa, INEC na da kwarin gwiwar cewa za a kirga kuri’u kamar yadda aka gabi a zabukan da suka gabata a jihohin Ekiti da Osun.
A WANI LABARIN KUMA: Najeriya Ba Tada Matsalar Talauci Da Tsaro, Sai…. Inji Obasanjo
Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, Darakta Janar na kungiyar kasuwanci ta duniya, Dr Ngozi Okonjo-Iweala, da kuma tsohuwar shugabar kungiyar lauyoyin Najeriya, Olisa Agbakoba, da wasu fitattun ‘yan Najeriya sun samar da hanyoyin magance kalubalen da kasar ke fuskanta.
Sun yi magana a ranar Asabar a bikin cika shekaru 113 na Kwalejin King. Kungiyar tsofaffin yara maza ta King’s College ta shirya taron mai taken ‘Gina Najeriya ne burinmu.’