Majalisar zartaswar kungiyar malaman jami’o’i ta kasa na shirin ganawa nan ba da dadewa ba domin tattaunawa kan basukan albashin ma’aikata na watanni takwas.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta tattaro cewa Duk da cewa majalisar zartaswar kungiyar ta kasa ba ta yanke ranar taron ba, shugaban ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke ya tabbatar wa da jaridar PUNCH cewa nan ba da dadewa ba za a dauki ranar da za a sanar da jama’a.
KARANTA HAKANAN Da Yiwuwar Kungiyar Malaman Jami’o’i ASUU Ta Shiga Sabon Yajin Aikin
“Mu (NEC) mun hadu a baya kuma mun cimma matsaya amma za mu sake haduwa don yanke shawara kan mataki na gaba da za mu dauka, kuma idan muka yi haka za mu sanar da jama’a.
“Amma abin da zan iya tabbatar muku shi ne nan ba da jimawa ba za mu gana, kuma za mu yanke shawara kan wannan batu na albashin da aka hana. Dole ne gwamnatin ta biya wadannan basussukan dimin hakkinmu ne.
“Mun bai wa gwamnati wani lokaci don ganin ko za a samu ci gaba, amma ba su yi komai ba. Muna tattara rahotanni daga mambobinmu kuma za mu dauki mataki,” inji shi.
Yayin da yake kokawa kan lamarin, ya ce malaman jami’o’in Najeriya na cikin mawuyacin hali.
“Mambobinmu suna cikin mawuyacin hali yayin da suke aikin da gwamnatin tarayya ta ce ba su yi ba kuma ba za a biya su albashi ba.
“Muna yin wadannan duk domin amfanin kasa amma hakan ba zai kasance har abada ba. Tabbas za mu gana nan ba da jimawa ba kuma za mu yanke shawarar da ta dace a wannan taron,” in ji shi.
Ya ce babu wata hanyar tattaunawa tsakanin malaman da gwamnatin tarayya, yana mai cewa za a ci gaba da fafatawa a tsakanin su a watan Fabrairu.
Jaridar SOLACEBACE ta rawaito cewa Shima da yake magana akan hana albashin malamai, Shugaban ASUU na Jami’ar Legas, Dakta Dele Ashiru, ya ce ya kadu matuka da har yanzu Gwamnatin Tarayya ba ta koma kan lamarin ba.
A Wani Labarin Kuma Sanata Uba Sani Ya Halarci Daurin Auren Yar Sarkin Zazzau Ambasada Ahmad Bammali
Dan takarar gwamnan jihar Kaduna Sanata Uba Sani ya bayyana farin cikinsa da halartar taron aurin auren Yar Sarkin Zazzau Ambasada Ahmad Nuhu Bammali.
Wannan na cikin sakonsa na fatan alkhairi ga ma’auratan wanda ya aikewa Jaridar DIMOKURADIYYA a safiyar yau.