Akalla gidaje biyar ne suka rushe sakamakon zaizayar kasa da ya auku a garin Auchi babbar hedikwatar karamar hukumar Etsako-West a jihar Edo a ranar Asabar.
Majiyarmu da ya halarci wurin da lamarin ya auku a ranar Lahadi, ya tabbatar da cewa da yawan gidaje ma a yankin gab suke da rushewa. Bayanai sun nuna cewa yankin Ekhei da kuma bangaren ma’aikatar ruwa zaizayar kasar ya fi shafa, wanda wannan zaizayar kasar ya zama shi ne babban barazana a yankin Auchi din.