A mako mai zuwa shugaban kasa zai dauki tsattsauran mataki zaman gida da ake ci gaba da killa mutane a gida a wani mataki na dakile yaduwar cutar Koronabairos a Nijeriya. Shugaban Cibiyar dakile cututtuka masu yaduwa ta Nijeriya, Dr. Chikwe Ihekweazu shi ne ya tabbatar da hakan a garin Katsina a yayin da ya kai wa gwamna Masari na Katsina ziyara domin ganewa idonsa irin shirin da jihar ta yi wajen yaki da Koronabairos.
Jaridar Daily Trust ta samu muryar zaman da aka yi, inda ta wallafa cewa; shugaban kasar ya shirya yin zama da gwamnonin domin tattaunawa akan daukar wadansu matakan. “Akwai wadansu tsattsauran matakai da za a dauka wanda zai shafi tattalin arziki, dangane da abin da za a taba da wanda ba za a tab aba.” Inji Chikwe.
Ya ci gaba da cewa; maganar gaskiya shi ne ba za a iya komawa yanayin da ba kafin Korona da kuma kafin a fara killace mutane a gida, za a yi dan wasu gyare-gyare akan yadda ya kamata a gudanar da wadansu lamura, dangane da yadda za a yi aiki, ibadodi, hutawa da wadansu harkokin kasuwanci. Wadannan duk matakai ne masu tsauri da ya kamata a tattauna.
“Har sai mun samu magani, wannan aikin ban a mutum guda bane, kowacce kasa na fama da wannan, dole ne a samu yanayin daidaito, domin ci gaban tattalin arziki domin al’umma su rayu. Ba za mu iya rufe komai ba.”
A na shi bayanin, gwamna Masari ya nuna damuwa na yadda matasa daga Katsina suka karkasu a jihohin kasarnan domin sana’o’i, musammana Legas, Fatakwal da Abuja, inda a halin yanzu suke dawowa gida, suna shigowa Katsina ta hanyoyi daban-daban saboda fadin kasa duk da kuma dokar hana shigowa da aka sanya.
Sai dai ya ce gwamnatinsa ta tattauna da Sarakuna domin bankado irin wadannan mutane a kuma killace su na kwana 14. Ya ce wadanda kuma suke dawowa ta kofar shiga gari, an dauki bayanansu tare da killace su na kwana 14.