Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara a ci gaba da gudanar da bincike da ceto wadanda suka fada hannun masu garkuwa da nutane a fadin jihar, yanzu haka rundunar ta yi nasarar ceto wasu mutane biyu (2) da aka yi garkuwa da su ba tare da wani sharadi ba ko biyan kudin fansa ba, a gundumar Magami da ke karamar hukumar KAURAN NAMODA.
Mai magana da yawun rundunar SP Muhammad Shehu ne ya sanar da hakan cikin wata sanarwa da ya aikowa da jaridar Dimokuraɗiyya a yammacin yau Alhamis.
DUBA WANNAN LABARIN: Kotu ta bayar da umarnin Tsare Ɗan Sarauniya kan zargin bata sunan Gwamnan Kano
SP Shehu ya kara da cewa An ceto wadanda lamarin ya rutsa da su a yayin wani gagarumin aikin bincike da ceto da aka gudanar a dajin Dumburum da Gidan Jaja a karamar hukumar Zurmi. Wadanda aka ceto din suna nan ana cigaba da kula da lafiyar su, kamar yadda rundunar ta sanar tun a baya.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Ayuba N. Elkanah psc+ ya jajanta wa wadanda abin ya shafa kan wahalhalun da suka sha a cikin tsawon lokacin da suka shafe a tsare. Ya kuma tabbatar wa al’ummar jihar cewa, ‘yan sanda tare da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaro da gwamnatin jihar za su ci gaba da aiki tukuru domin ganin an ceto duk wadanda aka yi garkuwa da su ba tare da wani sharadi ba a fadin jihar.
CP ya kuma yi kira ga jama’a da su ci gaba da baiwa jami’an tsaro goyon baya a ci gaba da gudanar da ayyukan yaki da ‘yan fashi da makami da sauran miyagun ayyuka a jihar.
Comments 1