Kwamishinan yan sandan jihar Zamfara CP Kolo Yusu ya jagoranci tawagar jami’an yan sanda na musamman inda suka kai ziyara wasu daga cikin manyan makarantu a jihar.
Jaridar Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa makarantun da kwamishinan ya ziyarta sun hada da Jami’ar Gwamnatin Tarayya dake Gusau, Kwalejin horas da malamai ta tarayya, da kuma makarantar sakandire ta jami’an yan sanda dake Gusau.
KARANTA ANAN: Jihar Nassarawa da ta rabauta da sabon Kwamishinan yan sanda
Wata Sanarwa da mai magana da yawun rundunar yan sandan Zamfara SP Muhammad Shehu, ya aikewa da Dimokuraɗiyya ya ce ziyarar an yi ne domin karfafa tsaron dalibai da Ma’aikatan makarantun.
Wannan dai wani bangare ne na umarnin da babban Sufeton Yan sandan kasar nan Usman Alkali Baba ya bayar, cewa a tabbatar da tsaro a duk Makarantun fadin kasar nan, domin dalibai su samu damar yin karatu cikin kwanciyar hankali.
A yayin ziyarar kwamishinan ya gana da shugabannin makarantun, tare da zagayawa da shi cikin makarantun domin ganin yanayin da aka samar don tabbatar da tsaro.
Yayin zagayen CP Kolo ya basu shawarwari dangane da yadda zasu iya kara inganta tsaron, bayan da ya kammala ganin komai tare da nazarin su.
Daga nan sai shugabannin makarantun suka godewa Kwamishinan bisa wannan ziyara da ya kai musu, suna masu yabawa da hazakar Kwamishinan wajen nuna kulawa ga halin da Makarantun ke ciki.
Kwamishinan yan sandan ya tabbatar musu da ci gaba da basu duk kulawar da ta kamata, domin ganin daliban sun ci gaba da samun kulawa da kwanciyar hankalin samun abinda suka je Makarantar domin aiwatarwa.
A wani labarin kuma: PDP Ta Karyata Rahoton Sauya Shekar Mambobinta 1, 500 A Jigawa
Jam’iyyar PDP reshen jihar Jigawa, a ranar Laraba ta karyata labarin da wasu kafafen yada labarai suka yada cewa kimanin mambobinta 1,500 ne suka sauya sheka zuwa jam’iyyar APC mai mulki.
Isa Bello Gwadayi, Sakataren jam’iyyar ya bayyana rahoton a matsayin karya.