Jam’iyyar PDP a jihar Zamfara ta sanya ranar Juma’a (gobe) domin sake gudanar da zaben fidda gwani na takarar gwamna a jihar.
A ranar Juma’ar da ta gabata, wata babbar kotun tarayya a jihar ta soke zaben fidda gwani na takarar gwamna na jam’iyyar da Alhaji Dauda Lawal Dare wanda ya lashe zaben fidda gwanin.
To sai dai bisa dalilin saba ka’idojin kundin tsarin mulkin jam’iyyar na daga cikin dalilin da ya sanya kotun soke zaben, bayan tsohon dan majalisar tarayya Alhaji Ibrahim Shehu Gusau, ya roki kotu da ta soke zaben da ya ce yana cike da kura-kurai.
KARANTA ANAN: Atiku Ya Rasa Wani Mataimaki Na Kusan Da Shi
Shugaban jam’iyyar na jihar, Alhaji Ahmad Sani Kaura, ya ce an kammala shirya gudanar da zaben fidda gwani a jihar cikin kwanciyar hankali, inda ya kara da cewa za a samar da daidaito ga duk wanda ya tsaya takara.
A wani labarin kuma: Dalibai Za Su Wadata Da Tallafin Karatu Idan Na Zama Shugaban Kasa – Kwankwaso
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Rabi’u Musa Kwankwaso ya yi alkawarin bayar da tallafin karatu ga daliban Najeriya a matakai daban-daban na ilimi idan aka zabe shi shugaban kasa a 2023.
Kwankwaso ya bayyana hakan ne ta shafin sa na Twitter da aka tabbatar a ranar Laraba yayin da yake ba da labarin tayin ilimi kyauta da ya bayar lokacin yana gwamnan jihar Kano.