Wani dan asalin jihar Zamfara kuma dan kasuwa Alhaji Mohammed Modi ya koka kan yadda kashe-kashe da sace-sacen jama’a da nakasa ‘yan kasa a jihar ya zama abin kunya da daure kai.
A wata tattaunawa ta musamman da ya yi da DAILY POST a Gusau, babban birnin jihar, Modi ya bayyana cewa ba a san takamaimai abin da wadannan ‘yan fashin ke bukata ba, yana mai nuni da cewa duk kokarin da ake yi na ganin sun yi hankoro da mika makamansu ya ci tura.
KARANTA WANNAN LABARIN: ‘Yan Bindiga Sun Afkawa Masu Ibada Suna Tsaka Da Sallar Juma’a Tare Da Hallaka 13
“Gwamnatin jihar ta fara tattaunawa da ‘yan bindigar domin su rungumi zaman lafiya amma sun ki amincewa da matakin sulhu da gwamnati ta dauka.”
“Yanzu, babu wanda ke da ‘yancin yawo a cikin jihar, ko da da rana tsaka saboda mutane na tsoron a kashe su ko kuma a sace su.”
A cewarsa, “Gwamnatin jihar ta dauki matakan tsaro daban-daban domin kame wadannan munanan ayyuka amma abin ya ci tura.”
Sannan ya koka da yadda jami’an tsaro na iya bakin kokarinsu amma daga dukkan alamu ‘yan ta’addan sun fi jami’an tsaro tsari da karfi a jihar.
Modi ya ci gaba da bayanin cewa hanya daya tilo da za a kawo karshen kashe-kashe da sace-sacen jama’a a jihar ita ce gwamnatin tarayya da na jihohi su nemo hanyar tallafa wa wadannan miyagu da ke aiki a jihar.
“Duk wadannan matakan tsaro ba za su taba magance matsalolin ba, har sai gwamnatin tarayya da na jihohi sun dawo hayyacinsu ta hanyar fallasa manyan laifukan da ke haddasa ayyukan ‘yan fashi a jihar.”
“Kamar yadda kuke gani, ’yan kasuwa da yawa suna gudun hijira zuwa wasu jihohi saboda rashin tsaro, kuma ba za ku iya zargi kowa da gudu don ceton ransa ba.”
“A yanzu haka na samu rahoton cewa an kashe wasu ‘yan sanda a yankin Shinkafi na jihar wanda aka ce harin ramuwar gayya ne biyo bayan harin bam da sojojin saman Najeriya suka kai a sansaninsu da ke yankin a makon jiya.”
“Haka nan a gundumar Bagega da ke karamar hukumar Anka ta jihar, an ce ‘yan bindiga sun mamaye kasuwarsu ta mako-mako, inda suka hana ‘yan kasuwa maza da mata yin sana’arsu ta halal.”
A wani labarin kuma, Za A Kawo Karshen Rashin Tsaro Kafin Karshen Shekara – Buhari Ya Bada Tabbaci
Za a kawo karshen rashin tsaro kafin karshen shekara, kamar yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tabbatar a Ile-Ife dake Osun, a ranar Asabar.
Ya ba da wannan tabbacin ne a wurin babban wasan karshe na 2022 Olojo Festival.