By Abbas Yakubu Yaura
Rahotanni sun bayyana cewa ‘yan bindiga sun rubutawa al’ummar Kirista a jihar Zamfara wasika, domin su rufe coci-coci ko kuma su fuskanci munanan hare-hare.
Kamar yadda SaharaReporters ta ruwaito, mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Mohammed Shehu, yace ‘yan sandan na sane da wasikar barazanar, inda ya kara da cewa “muna kan gaba wajen barazanar”.
DSP Mohammed Shehu yace, “Eh, zan iya tabbatar da cewa gaskiya ne, an aika da wasikar barazana ga Kiristocin Jihar Zamfara su daina ibada da tare da rufe Coci coci dake fadin jihar. Sannann kuma “ ‘yan sanda sun sanar da shugabannin Kirista game da barazanar.
“Haka zalika CP ya gayyaci shugabannin kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) a jihar domin tattauna matakan tsaro a kusa da kewayen coci-coci.
“A dangane da haka, CP ya samar da wata tawaga ta musamman domin yin sintiri tare da kare masu ibada, musamman a ranakun Lahadi.”Bugu da kari, an tura ma’aikatan sanye da kayan aiki don tattara bayanan sirri da kuma bankado wadanda ke da hannu a cikin wasikar barazanar,” in ji shi.
A ranar Lahadin data gabata ne wani shugaban addinin Kirista daya nemi a sakaya sunansa ya bukaci mabiya addinin Kirista a sassan duniya dasu yi addu’a kan halin da suke ciki a Zamfara da sauran sassan arewacin Najeriya.
Sannan yace, “Mu yi wa Kiristocin Arewacin Najeriya addu’a, musamman a Jihar Zamfara saboda an ba mu wa’adin shekaru uku na rufe dukkan coci-coci dake Jihar.
“An sanya sunayen wasu coci-coci da za a kai hari a tsakanin yanzu zuwa karshen watan Disamba, kodayake coci-cocin da za a kai wa hari a cewar kungiyar Fulani data rubuta wasikar suna wajen garin, amma mun yi imanin cewa dabara ce kawai.
“An kuma kwafi wannan wasika zuwa ga ‘yan sanda, jami’an tsaro na DSS da hukumar tsaro ta farin kaya (NSCDC) da sauran hukumomin tsaro duk sun tabbatar da samun takardar.
“Rundunar ‘yan sanda a jihar ta umurci Kiristoci da su kara tsaurara tsaro a duk wuraren ibada, gidajen fastoci, da sauran cibiyoyin kiristoci.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa “Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) a jihar Zamfara ta kuma umarci dukkan coci-coci da kada su gudanar da ayyukan coci fiye da karfe 5 na yamma na tsawon watanni uku masu zuwa,” in ji shi.
Kamar yadda al’amura ke tafiya, wasu Kiristoci na tunanin barin Jihar Zamfara zuwa yankunan da suke da tsaro.