By Abbas Yakubu Yaura
Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta samu nasarar kwato bindigu guda takwas bayan sun kai farmaki a unguwar ‘yan bindiga dake kusa da Bayan Ruwa a karamar hukumar Maradun.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Ayuba Elkanah, wanda ya bayyana haka a ranar Laraba, yace farmakin jami’an ‘yan sandan ya biyo bayan samun bayanan sirri da aka samu.
“Jami’an sun yi arangama da ‘yan bindigar inda suka kashe da yawa daga cikinsu yayin da wasu suka tsere da raunukan harbin bindiga.
Sannan ya kara da cewa, “A yayin da ake binciken inda lamarin ya faru,sun kwato bindigogi kirar AK-47 guda takwas (8),da wata Bindiga guda daya kirara (GPMG), da makamin roka daya, da kuma albarusai guda biyar, wadanda ‘yan sanda suka kama.”
Elkanah ya kuma ce rundunar ta dakile wani hari da aka kai kauyen Rughar Tudu a lokacin da ‘yan bindiga suka farwa al’umma tare da yin garkuwa da mutane uku.inda yace an ceto mutanen uku da aka yi garkuwa da su ciki har da wani jariri dan wata 3.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa jami’an ‘yan sandan sun kwato shanu 69 bayan wani artabu da suka yi a kauyen Tudun Masu dake karamar hukumar Bungudu wanda 60 daga cikin su aka mayar dasu zuwa ga mamallakan su na asali.