Kociyan kungiyar kwallon kafa ta Manchester City, Pep Guardiola, ya bayyana cewa ya na fatan zasu doke Tottenham a wasa na biyu da zasu fafata a sati mai zuwa a gasar cin kofin zakarun Turai bayan sunyi rashin nasara a wasan farko a birnin Landan. Har ila yau, Pep Guardiola, ya jaddada cewa, ko kadan bai damu da caccakar da ake yi ma sa na gaza samun nasara akan kungiyar Tottenham a fafatawar da kungiyoyin biyu suka yi a gasar cin kofin zakarun Turai, in da suka ta shi 1-0. A martanin da ya mayar, mai koyarwa Guardiola ya ce, masu zaton Tottenham za ta zura kwallaye uku a ragar Manchester City a ranar ta Talata, sun yi kuskure duk da cewa Tottenham babbar kungiya ce kuma da shahararrun ‘yan wasa kuma yana ganin zasu samu nasara mai rinjaye idan anje gidansu. Guardiola ya ce, duk da dai gasar zakarun Turai na a matsayin wani buri da ake son cimma, amma samun nasara ba abu bane mai sauki, yayin da ya kara da cewa, bai zama dole kungiyar ta rika kai matakin wasan karshe a kowacce shekara ba saboda kowacce kungiya yanzu tanada karfi. Dan wasa Son ne dai ya zura kwallo daya tilo wadda tabawa Tottenham din nasara a wasan sai dai tun farkon wasan Manchster City ta zubar da damar cin kwallo bayan da dan wasa Sergio Aguiro ya zubar da bugun fanareti. Yanzu haka a ranar 18 ga watan Aprilu ne kungiyoyin biyu za su sake fafatawa da juna a zagaye na biyu na gasar a filin wasa na Ettihad dake garin Manchester yayinda Manchester City take bakatar zura kwallo sama da daya idan har tana bukatar tsallakewa zuwa mataki na gaba. Ita ma dai Liberpool ta lallasa FC Porto da ci 2-0 a gasar ta zakarun Turai kuma Wannan nasarar ta bai wa Liberpool kwarin gwiwar samun gurbi a matakin wasan dab da na karshe a gasar sai dai itama FC Porto zata karbi bakuncin Liberpool din itama a sati mai zuwa.