Kwamishinan yan sandan jihar Kaduna Mr Mudasiru Abdullahi ya bada Umarnin gudanar da cikakken bincike kan wadanda suka kashe matukin jirgin saman Nigeria Mr Abdulkari ibn Na-Allah.
Abdullahi ya bada wannan umarnin a yammacin jiya Lahadi a garin Kaduna, cikin wata sanarwa da jami’in Hulda da jama’a na rundunar APS Mohammed Jalige ya fitar.
“Na bayar da umarnin a gudanar da cikakken bincike tare da nufin bankado wadanda suka aikata laifin, da kuma gurfanar da su gaban kuliya,” kamar yadda Kwamishinan ya bayyana a cikin sanarwar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamna Lalong ya sassauta dokar Hana fita a Jos
Kazalika ya ce, “Rahoton ya nuna mana cewa, masu kisan gillar sun kutsa kai cikin gidan matukin jirgin a titin Umar Gwandu dake garin Malali, na Nan jihar Kaduna cikin dare, inda suka shake shi har lahira, sannan suka tafi da motar sa kirar Lexus SUV zuwa wani wurin da ba a san ko inane ba,” inji sanarwar.
Kazalika rundunar yan sandan ta yi kira ga al’uma baki daya, dasu taimakamata da bayanan da za su iya taimakamawa wurin binciko wadanda suka yi kisar gillan.
Comments 1