Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa hukumar karben koke-koke da yaki da cin hanci zata ci gaba bincikar Sunusi, sakamakon biyo bayan dama da kotu ta bawa hukumar na bincikarsa.
“Lokacin da muka so kawo gyara a masarauta, tsohon sarki yaki aminta tare da bada hadin kai, wanda yake ganin gara ya bar sarautar da ya aminta da kudurinmu”.
Ganduje ya bayyana haka ne a yayin da yake ganawa da manema labarai a dakin taro na ‘Africa house’ dake gidan gwamnatin jihar.
Ya kara da cewa a lokacin da suka so bincikiar sarkin, ƙungiyar dattawan Kano su ne suka kawo cikas a lamarin amma a yanzu kotu ta bada dama kuma komai zai ci gaba.
Tsohon sarkin dai ya kai ƙarar hukumar karben koke-koken da yaki da cin hanci, akan bincike da suke buƙatar gudanarwa akan, sai dai wata kotu ta bawa gwamnatin Kanon dama da ci gaba fa binciken.