Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje yace gidauniyar bunkasa addinin musulunci ta Ganduje wato (GANDUJE FOUNDATION), zata ci gaba da mayar da hanKali wajen ganin ta bunkasa sha’anin neman ilimin addini da na zamani a fadin jihar Kano.
Gwamnan ya bayyana hakan yayin bikin rufe musabakar alqur’ani ta bana karo na Ashirin da daya da ya gudana a rufaffen dakin taro na filin wasa dake Kofar Mata a jihar Kano.
Gwamna Ganduje ya hori al’umma da su kara zage dantse wajen neman ilimi, yana mai cewa gidauniyar karkashin kulawar sa zata ci gaba da aikin musulumtar da maguzawan dake zaune a sassan jihar nan.
KARANTA ANAN: An Samu Sauƙin Kiran Waya Don Karbar Kudin Fansa – Pantami
A yayin taron na Asabar din nan, an raba kyaututtuka ga wadanda suka samu nasara, inda aka baiwa wanda yazo na daya a rukunin izifi arba’in Mujahid Jibril daga karamar hukumar Bunkure Kyautar motar hawa kirar Honda da kujerar hajji, yayin da na biyu Anwar Musbahu Ali Fagge ya rabauta da baburin adaidata sahu, sai na uku da ya samu Firinji da kuma keken dinki.
Da suke jawabi wadanda suka samu nasarar sun godewa Gwamna Ganduje tare da yin kira ga matasa su rungumi dabi’ar neman ilimi.
Manyan bakin da suka halarci wurin taron sun hada sarkin karaye Alhaji Ibrahim Abubakar na biyu da kuma wakilan sarakunan Kano.
A wani labarin kuma: Yajin Aikin ASUU: NANS Tayin Barazanar Rufe Filayen Jiragen SamaN Najeriya
Biyo bayan takun saka tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyar malaman jami’o’i ta ASUU na tsawon watanni bakwai, kungiyar dalibai ta kasa NANS ta bayyana aniyar ta na dakatar da aiki a dukkan filayen jiragen sama na kasa da kasa.
Kungiyar NANS ta kasa ta yi taro a karshen mako a Akure, babban birnin jihar Ondo, inda ta yi Allah-wadai da yadda gwamnatin tarayya ke mu’amala da malaman da suke yajin aiki da kuma ilimi gaba daya.