Gwamnatin tarayya a ranar Talata ta jaddada dokarnan ta haramta shigo da shinkafa ta iyakokin kasarnan.
Abdulhamid Ma’aji, Kwanturola na hukumar Kwastan mai lura da yankunan Sakkwato da Zamfara shi ne ya tabbatar da hakan a yayin da suke bude iyakar Illela dake Sakkwato.
Gwamnatin tarayya ta ce ta jaddada wannan dokar ne yadda suka ga mutane masu shiga da fita ta wannan iyakar na murnar bude iyakar.
An dai bukin bude iyakar ne a tsakanin jami’an Nijeriya da Jamhuriyyar Nijer. Ma’aji ya ce za su ci gaba da sanya ido akan iyakar domin tabbatar da doka da oda.