Daga Muhammad Gambo Damaturu
Gwamnan Jihar Yobe, Alhaji Mai Mala Buni ya yabawa jami’an hukumar sojin Nigeria dake aiki a karkashin rundunar “Operation Hadin kai” bisa kokarinsu wajen wanzar da zaman lafiya a yankin arewa maso gabashin Kasar.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Gwamnan yayi wannan yabo ne a ranar Asabar, 1 ga watan Octoban shekarar 2022.
A jawabinsa ga jami’an tsaro na murnar cikar Najeriya shekaru 62 da samun ‘yancin kai.
KARANTA ANAN: Yan Bindiga sun sace basaraken gargajiya da matarsa
Gwamnan yace bikin bada lambar yabon da hukumar soji ta shirya a wannan rana, yana da matukar muhimmanci domin kuwa zai nuna jinjina ga jami’an rundunar, wadanda suka mika wuya tare da jajircewa wajen samar da zaman lafiya.
Gwamna Mai Mala Buni, wanda mai bashi shawara kan harkokin tsaro, Burgediya Janar Dahiru Abdus-Salam (Rtd) ya wakilta a bikin ya ce jajircewan sojojin da sauran jami’an tsaron ne ya samar da yanayin gudunar da ayyukan ci gaba da ake ciki yanzu.
Tun da farko da yake jawabin maraba, Kwamandan rundunar sojin hadaka, rukuni na biyu, (Sector 2 Joint Task Force Operation Hadin Kai), Major Janar Koko Isoni yace wannan biki ya dade hukumar soji tana yinsa domin nuna yabo da godiya ga jami’an da suka yi aikin kwazo da bajinta.
Ya kara da cewa, ana yin bikin ne domin nuna soyayya, bada tallafi, da kuma dada karfafawa jami’an soji kan sadaukar da ‘yancinsu da suka yi don yiwa kasarsu aiki.
Daga bisani ya yabawa Gwamnatin jihar Yobe karkashin jagorancin Gwamna Mai Mala Buni saboda kasancewar ta masauki ga jami’an soji dake rundunar Operation hadin kai.
Manyan Jami’an Gwamnatin Jihar Yobe da hukumomin tsaro daban-daban ne suka halarci bikin.
A wani labarin kuma: Magoya bayan Obi Sun Kalubalanci Yan Sandan Jihar Legas
Dubban matasa ne a ranar Asabar suka yi dafifi a Legas domin taron gangamin mutum miliyan 4 na dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party (LP), Peter Obi.
Magoya bayan sun bijirewa dokokin da aka sa a safiyar ranar da kuma tsaro na gudanar da taron a sassan Legas.