Gwamnatin Kano ta bayyana cewa rage albashin ma’aikata da aka yi a watan Nuwamba da Disambar 2020 ba na dindindin bane.
Malam Muhammed Garba, Kwamishinan yada labaran Kano ne ya tabbatar da hakan a cikin sanarwar da ya fitar a ranar Alhamis a Kano.
Garba ya tabbatar da kudurin gwamnati wajen tabbatar da biyan mafi karancin albashi na naira dubu 30 ga ma’aikatan jihar. A cewarsa rage albashin a watannin Nuwamba da Disamba ba mai dorewa bane, inda ya ce hakan ya faru ne sakamakon ragin da aka samu daga kudaden da gwamnatin tarayya ke bai wa jihar sakamakon annobar cutar korona.
Ya ce an rage albashin ne saboda hakan zai taimakawa gwamnati wajen ci gaba da ayyukanta a daidai lokacin da ake fama da matsalar durkushewar tattalin arziki da ake fuskanta a kasarnan. Ya ce gwamnati ta dauki wannan matakin ne sabanin zabar biyan rabin albashi ko kin biyan albashin ko a biya wasu a hana wasu a jihar.