)
Daga mustapha Musa sarkinfawa.
Hukumar dake kula da sufurin jiragen kasa ta kasarnan wato ‘Nigerian Railway Corporation (NRC)’ a turance tace zata dawo da jigilan fasinjoji matafiya daga Abuja zuwa Kaduna.
Wannan dai na zuwane kasa da awanni 24 bayan dakatar da aikin sakamakon harin da aka kaiwa jirgin,wanda ya tilastawa hukumar dakatar da aikace aikacen ta daga kaduna zuwa Abuja.
Hukumar dai ta bayyana shirin dawo da aikinne a wata sanarwa data fitar jiya juma’a.
Jaridar dimokuradiyya ta gano cewa hukumar ta gyara shashin daya lalace na jikin jirgin sakamakon harin wanda hakan ya bata damar dawowa cigaba da aikin.
KARANTA WANNAN LABARIN: Abin da yasa nake Tsinuwa a Cikin Fim, Inji Musa Mai sana’a
“Muna farin cikin sanar da dukkan al’umma cewa a yau asabar ashin da 23 ga watan oktoba shekarar 2021,jigi zai cigaba da zirga zirga kamar yadda ya saba daga kaduna zuwa Abuja,”
“jirgimu zai cigaba kamar yadda aka saba, daga IDU, Abuja zai tashi karfe 9:50.na safiya,sannan kuma daga RIGASA, Kaduna karfe 10:35 na safiya, akarshe muna baiwa jama’a hakuri bisa tsaikon da aka samu,muna godiya da juriya da addu’o’in ku inji hukumar ta Railway”
A wani labarin Kuma na daban.
Gwamnatin jihar Borno tace za ta rufe dukkan sansanonin ‘yan gudun hijira dake cikin Maiduguri, zuwa ranar 31 ga watan Disamba.
Gwamna Babagana Zulum ya bayyana haka lokacin da yake zantawa da manema labarai na fadar gwamnati a karshen wata ganawar sirri da yayi da Shugaba Muhammadu Buhari, a Abuja ranar Juma’a.
Yace an yanke shawarar rufe sansanonin dake Maiduguri ne sakamakon ci gaban da aka samu a yanayin tsaro a jihar.
A cewarsa, gwamnatin jihar ta yanke shawarar rufe sansanin don baiwa wadanda suka rasa muhallinsu damar komawa gidajen kakanninsu.inda ya kara da cewa”Na zo ne don yi wa shugaban kasa bayani kan kokarin da gwamnatin jihar Borno ta yi wajen tabbatar da dawo da ‘yan gudun hijira zuwa gidajensu.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Gwamnan, ya kammala shirye -shiryen dawo da mutanen da suka rasa muhallansu zuwa makwabtan Nijar da Jamhuriyar Kamaru, tare da hadin gwiwar Ma’aikatar Agaji ta Tarayya.”Bugu da kari, a ranar 27 ga watan Nuwamba, gwamnatin jihar Borno zata tabbatar da sake tsugunar da ‘yan gudun hijirar dake zaune a lardin Diffa na Nijar zuwa karamar hukumar Malumfatari, ta jihar Borno inda bamu da yawan mutane saboda tashin hankalin,” in ji shi.
Kazalika yace, “Don haka, sojojin Najeriya suna bayar da duk tallafin da ake buƙata ga gwamnatin jihar Borno.” Ina farin cikin sanar da ku kuma cewa Babban Hafsan Sojojin Ruwa, Rear Adm. Awwal Gambo, ya tabbatar da dawowar Sojan Ruwa. Base zuwa Baga a watan daya gabata. ”