Mataimakin shugaban Ƙasa Yemi Osinbajo yace shirin shirin Hukumar zuba hannun jari na ƴan Najeriya mazauna ƙasashen waje wato- NDIS na ɗaya daga cikin wata kafa da zata kawo zuba jari a Ƙasar.
Osinbajo ya bayyana haka a lokacin taron Hukumar cigaban ƴan Najeriya mazauna ƙasashen waje NDIS karo na 4 na shekarar 2021.
KARANTA WANNAN LABARIN: An soke lasisin hakar ma’adinai 1,566 a shekarar 2021 – Minista
Mataimakin Shugaban Ƙasa yace hakan zai sanya a fitar da ƴan Najeriya Miliyan 25 daga ƙangin Talauci a shekarar 2025.
Taron ya wakana a ranar Talata a ɗakin taro na shugaban ƙasa dake Villa Abuja.
Osinbajo Wanda ya samu wakilcin Sakataren Gwamnatin Tarayya Boss Mustapha yayi nuni dacewar an ƙirƙiri NDIS domin samar da zuba hannun jari a Najeriya.
Osinbajo ya bayyana cewar manufar Gwamnatin Buhari shine a inganta kuɗaɗen shiga a ƙasar.
Yace gwamnatin a shirye take domin samar da ayyukan yi.