Hukumar lura da jindadin alhazai ta jihar Kwara ta bayyana za a hana marasa lafiya zuwa hajjin 2020. Hukumar ta jaddada cewa wadanda suka daura niyyar zuwa aikin hajjin 2020 a kasar Saudiyya, idan har aka gano ba su da lafiya, ba za a bari su tafi ba.
Alhaji Mohammed Tunde-Jimoh, Sakataren gudanarwar hukumar shi ne ya bayyana hakan a ranar Litinin a garin Ilorin, jim kadan da kammala taro tare da jagororin shirya ayyukan Hajjin daga kananan hukumomi 16 a jihar.
Har wala yau zaman, ya samu halartar jami’an hukumar hajjin da suke yiwa masu niyya rijista a jihar, inda suka tattauna batutuwa daban-daban dangane da Hajjin 2019 tare da shirya ma Hajjin 2020.
Sakataren gudanarwar ya ce; dakatar da wadanda suka kasa gabatar da shaidar koshin lafiya za a yi hakan ne saboda kare su daga irin fadi rashin da ake yi a yayin ibadar Hajji, wanda ya ce hakan na iya sanya rashin lafiyarsu ya sake tabarbarewa wanda hakan ka iya haifar da mutum ya rasa ransa.
A don haka ya shawarci daidaiku da ma kungiyoyi wadanda suke son daukar nauyin maniyyata hajjin 2020 da su tabbatar da ingancin lafiyar mutum kafin su dauki nauyi.