Ƙasar Rasha ta jaddada aniyar ta , ta kara faɗada alaƙar difolmasiyar da ke tsakanin ta da Koriya ta Arewa.
Shugaban kasar ta Rasha Vladimir Putin ne ya tabbatar hakan.
A wata sanarwa da ya aikawa takwaransa Kim Jong’un a bikin ranar yancin kai Koriya ta Arewa, shugaba Putin ya ce matakin zai zama mai amfani ga kowane ɓangare.
Kasar Sin Ta Jaddada Kudurinta Na Ci Gaba Da Hulda Da Kasashen Afirka
A nasa bangaren, Mr Kim ya ce kawance tsakanin kasashen biyu ya kullu ne tun a yakin duniya na biyu, inda kasar tayi nasara akan kasar Japan.
Ya ƙara da cewa dangantaka tsakanin kasashen biyu zata karu sosai nan ba da jimawa ba.
Kamar yadda kafar yada labarai kasar ta rawaito ta ce, Shugaba Putin ya ce alaƙar difolmasiya za ta yi dai dai da bukatun kasashen biyu.
A tashi sanarwa Mista Kim ya kara da cewa matakan da hadin kai da taimakon juna da nuna goyon baya da ke tsakanin kasashen biyu ya kai wani babban mataki, da ke iya magance fuskantar barazanar soji daga wasu ƙasashe da ke adawa dasu da kuma wasu shirye-shirye .
Ko da yake fadar gwamnati , Pyongyang ba ta bayyana sunayen sojojin da ta ke nufi ba, amma Koriya ta Arewa ta dade tana amfani da kalmar ga Amurka da kawayenta.
A baya dai Tarraya Sobiya ta kasence babbar kawa ga Koriya ta Arewa ta fuskar tattalin arziki , haɗin kai, al’adu da taimakon juna.
Amma dangantakar ta gamu da cikas kaɗan a shekarun baya, tun lokacin da Rasha ta nisanta daga yankin tun a farkon shekarun 2000.
A wantan Yulin da ya gabata, ƙasar Koriya ta Arewa ta kasance ɗaya daga cikin kasashen duniya da suka goyi bayan Rasha a yankunan da ta mamaye a gabashin Ukraine, bayan da Rasha ta bayyana su a matsayin masu cin gashin kansu.
Sai dai ana ta bangare , Ukraine da ke yaƙi da Rasha don kare iyakokin, ta katse dangantakar difolmasiya tsakanin ta da Koriya ta Arewa.