Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya bayyana cewa; gwamnatinsa ta dukufa wajen magance matsalar matsalar rashin aikin yi a tsakanin matasa a jihar.
Gwamna Abdullahi Ganduje ya bayyana hakan ne a yayin da kwamitin tsaro na kungiyar kamfen dinsa suka shirya wani zama a gidan gwamnati dake Kano a ranar Alhamis.
Ganduje ya ce; gwamnatinsa za ta ci gaba da bai wa matasa da mata muhimmanci, inda za su dukufa wajen ganin an bai wa matasa da mata ayyukan yi domin ganin sun dogara da kawukansu.