Gwamnatin jihar Oyo ta baiwa al’ummar garin Oyo tabbacin cewa sabon Alaafin na Oyo zai fito nan ba da dadewa ba, inda ta bukace su da su yi hakuri.
Gwamna Seyi Makinde ya bayar da wannan tabbacin ne a wajen addu’ar fidau wato kwana na takwas da aka gudanar domin karrama marigayi Oba Adeyemi a na fadar sa da ke Oyo.
Marigayi Oba Adeyemi ya rasu ne a ranar 22 ga watan Afrilu a asibitin koyarwa na jami’ar Afe Babalola, Ado-Ekiti.
Gwamns Makinde, wanda Chief Bayo Lawal, kwamishinan kananan hukumomi da harkokin masarautu ya wakilta, ya ce yana sane da cewa mutane sun kosa su samu sabon sarki.
Tun da farko a sakon gaisuwar su mabanbanta Imam Masud Ajokidero da Rev. Eyitayo Sulola, sun bukaci jama’a da su rika rungumar bin doka da oda kamar yadda marigayi Alaafin ya yi a lokacin da yake raye.
Sun yi kira ga sarakunan “Oyo Mesi” da su bi hanyar zaman lafiya ba don zuciya ba wajen zaben sabon sarki.