Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa; ta shirya raba gidan sauro har miliyan takwas a karkashin shirin gwamnatin tarayya na kawo karshen cutar Maleriya. Babban Sakataren ma’aikatar lafiya ta jihar, Alhaji Bala Muhammed, ya ce za su raba gidajen sauron ne kyauta ga al’umma cikin watan Oktoba.
Shugaban ma’aikatar lafiyar ya bayyana hakan ne a yayin wani taron wayar da kan jama’a ga kafafen watsa labarai kan yadda za a raba gidajen sauron da ya gudana a garin Kano.
Dr. Imam Wada, Babban Daraktan lura da lafiyar al’umma shi ne ya wakilci Muhammed, inda ya ce za su dauki matakin da ya dace wajen ganin sun raba gidajen sauron yadda ya kamata. Ya kara da cewa; amfani da gidan sauron yadda ya kamata yana daga cikin hanyoyi mafi sauki wajen kawo karshen cutar Maleriya.