Zamu tabbatar Ɗiyan ku sun samu ingantaccen Ilmi — Masari ga Al’ummar Jihar Katsina
Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari, Ya Jaddada Kudirin Gwamnatinsa na cigaba da baiwa ilimi fifiko a Jihar.
Alhaji Aminu Bello Masari ya bayyana haka a lokacin da ya halarci ƙaddamar da Ɗakin Kwanan Ɗalibai da aka sanya Sunan sa a Jami’ar Al-Hima Ilori.
Inganta fannin ilimi na da tarin lada mara iyaka da sadaukarwa.
KARANTA WANNAN LABARIN: Da Yuwuwar Mu Sayar Da Manchester United—-Iyalan Glazer
Gwamna Masari ya bayyana cewa babban kalubalen da ke tsakanin al’umma shi ne sadaukar da wani abu dake garesu don ganin sun tallafa wa ilimi.
Gwamnab ya nanata cewa dole mutane su tashi tsaye tare da yin wani abu dazai haɓɓaka dukkanin ilimomi.
Ya ce duk da cewa mutane na da bangarori da dama da suka fi ba da muhimmanci wajen bayar da gudunmawarsu, ya tunatar da su cewa babu wani fanni da ya fi dacewa da tallafi kamar na ilimi.
Don haka ya taya wanda ya assasa kuma shugaban kwamitin amintattu na jami’ar Al-hikma murna bisa irin dimbin jarin da zai samu da lada mara iyaka ko bayan rayuwarsa.
Taron na musamman da ya samu halartar manyan Malamai daga Jami’ar ya samu jagoranci Babban Limamin Cibiyar Dakta Kamaluddeen Ali Al-Mubarak.
Ana shi tsokaci mai ba Gwamna shawara kan ilimi mai zurfi Dakta Bashir Usman Ruwan Godiya shi ma ya jagoranci addu’ar Allah ya maido da zaman lafiya a jihar Katsina da yankin arewacin kasar nan da ma Najeriya baki daya.
Muhimman abubuwan da suka faru a zaman sun hada da gabatar da karatun Al-kur’ani.
Gwamnan ya kuma bayyana cewa gwamnatin jihar Katsina za ta dauki nauyin ’yan asalin jihar da suka cancanta su yi karatu a Jami’ar Al-Hikmah Ilorin daga wannan zangon karatu.