Shugaban Ƙasa Muhammad Buhari yasha alwashin tabbatar dacewa, muradun tsamo miliyan 100 daga ƙangin talauci an cimma shi a shekaru 10 masu zuwa.
Shugaban Ƙasar ya bayyana haka a jawabin da yiwa ƴan kasa na murnar cikar Najeriya 61 da samun ƴancin kai a Villa dake Abuja.
Acewar sa ta la’akari da nasarorin da aka cimmawa a shirye-shirye tallafawa, ya amince da ƙarin ɗaukar masu amfana da shirin N-Power daga dubu ɗari 500,000 zuwa miliyan 1,000,000, daga cikin haka mutane dubu 510,000 sun fara shirin, a yayinda ake cigaba da zaɓar saura mutane dubu ɗari 490,000 waɗanda zasu amfana da shirin wanda yake gudana a halin yanzu.
KARANTA WANNAN LABARIN: Muna aiki tuƙuru domin yiwa ƴan Najeriya rajistar katin zama ɗan ƙasa a shekarar 2022 — NIMC
Ya ƙara dacewa, shirin ciyar da Ɗalibai ƴan makaranta wanda aka ƙaddamar a faɗin jahohi 35 da babban birnin tarayya Abuja, an ɗauki sama da mata dubu 103,000 da aka ɗauka, domin dafa abinci a ƙarƙashin shirin, a yayinda kimanin yara miliyan 10 ake ciyar wa a faɗin ƙasar.
Shugaba ya kuma bayyana cewa ya bada umarnin a ƙara yawan mutanen da ake baiwa kuɗaɗen tallafi ya zuwa miliyan 1.
A wani Labarin kuma
Shugaban kwamitin kula da zirga zirgar ababen hawa na Apapa da mai ba da shawara ga Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Legas, kan Sufuri, Oluwatoyin Fayinka, ya baiwa direbobin manyan motoci wa’adin kwanaki bakwai, wadanda suka yi fakin ba bisa ka’ida ba a kan babbar hanyar Oshodi-Apapa, don cire motar in kuma ba haka manyan motoci za a kame su.
Wannan yazo ne yayin da kwamitin ya yarda cewa ana ci gaba da samun nasara a kokarin kubutar da Apapa daga tarnakin da manyan motocin suka sata a hankali.
Fayinka, wanda ya zanta da manema labarai, ya zargi direbobin manyan motocin da lalata ayyukan da tawagar keyi ta hanyar yin parking ba bisa ƙa’ida ba a kan titin, musamman kan titin Oshodi-Apapa, wanda hakan ya haifar da ƙulle hanyar baki daya da jefa masu ababen hawa cikin mawuyacin hali.
Fayinka ya yi gargadin cewa bayan karewar wa’adin tawagar za ta fara aiwatar da ayyukan ta gaba daya, yana mai cewa “Ba za a yi komai ba alfarma saniya. ”
“Akwai wata hanya da aka sadaukar domin duk manyan motoci su motsa amma abin da masu tafiya ke yi shine zasu je su hadu da wani a wani wuri inda suke da manyan motoci 50 daza su motsa sabanin kusan 10 zuwa 20 ana tsammanin za a motsa su lokaci guda.
Giwa ya kuma ce“Babu shinge a Apapa. Kafin yanzu, don ku motsa babbar mota, mutane sun biya kusan N150, 000 zuwa N200, 000 don matsar da babbar mota daga Ijora-Olopa zuwa tashar jiragen ruwa ta Apapa saboda an kafa ta ne da manhaja kuma duk abin da yake da hannu yana da tsoma bakin ɗan adam.
“Akwai manyan motoci a wannan hanyar suna jira su shiga ɗaya bayan ɗaya,” babban mutum “zai kira wani yace ina da manyan motoci 50 ina so su wuce. Akwai layin da aka keɓe don kowace motar ta wuce, don haka babban mutum zai hanzarta kuma za su kawo manyan motocin 50 su koma kan sauran layin dake da kyauta don sauran mutane su yi amfani da su.
Comments 1