Gwamnatin Amurka ta ce za ta taimakawa Najeriya a yakin da ta ke yi da ‘yan Yan bindiga a fadin kasar.
Mataimakin babban mai ba da shawara kan harkokin tsaro na Amurka, Jon Finer, ne ya ba da tabbacin hakan, a yayin da yake zantawa da manema labarai a Abuja babban Birnin Nigeria a jiya Litinin.
“Za mu bayar da taimako na fasaha don shirye -shiryen adalci, wanda akasarinsu an sadaukar da su ne don taimakawa Nigeria, ta yadda take samun koma baya a wannan lokaci na kalubalen ‘yan bindiga, kuma za mu ci gaba da ba da shirye -shirye irin wannan don taimakawa kasar,” in ji shi.
Dangane da muhawara mai cike da cece -kuce da fargabar Amurka game da yadda za a yi amfani da jiragen yaki na Super Tacuno, ya ce: “Ina tsammanin mun bayyana hasashen da muke yi kan yadda za a yi amfani da Jiyagen ta hanyar da ta dace”.
KARANTA WANNAN LABARIN: Sakon Sanata Uba Sani game da Ranar Mauludi
A kan Yan kungiyar Aware na IPOB, Finer ya ce, wakilai sun tattauna batun da Gwamnatin Nigeria tare da jaddada bukatar magance matsalar da ta haifar da kungiyar.
Comments 1