Gwamnatin tarayya ta ce za ta fadada tallafin da take bayarwa ga Talakawa ta hanyar amfani da ci gaban zamani da ya hada da BVN na asusun bankin mutum domin gano Talakawa domin tura musu tallafi.
Ministar Tallafi da jinkai, Sadiya Farouq ita ta bayyana hakan a Abuja a ranar Talata a yayin da take amsa tambayoyi ga kwamitin shugaban kasa kan dakile cutar Koronabairos.
Gidan Talabijin na CHANNELSTV sun labarto cewa Ministar ta tabbatar da cewa za su yi amfani da fasahar zamani wajen bada wannan tallafi, inda ta ce zai fi saukin isa ga wadanda dama sune muradin bada tallafin cikin sauki.
Ta ce; “Muna amfani da BVN da kuma lambar wayoyi domin gano Talakawa domin ba su wannan tallafin a cikin al’umma.” Inji ta.
Ta ci gaba da cewa; “wannan ya fi sauri, ya kuma fi zama cikin gaskiya, kuma zai fi saukin a yi bincike a kai.” Ta jadadda.
Sai dai ta tabbatar da cewa shirinsu na bi gida-gida suna rabawa Talakawa kudi a wadansu sassan kasarnan shi kansa ana bin ka’ida ne, kuma yana tafiya cikin gaskiya da tsari. Sannan ta ce gwamnatin tarayya ta bi dukkannin matakan da suka dace wajen ganin ba a maimaita tallafin ga gida daya ba.
Sannan ta ce Sarakuna da sauran kungiyoyin al’umma ana amfani da su wajen bankado Talakawan wajen ba su tallafin gwamnati.