Rundunar sojin ruwan Nijeriya sun yi alkawarin maganin duk wadansu barayin man fetur da iskar gas a Nijeriya. Ma’aikatar man fetur ta Nijeriya, wato NNPC tare da hadin guiwar jami’an sojin ruwa sun yi hadin hannu a tsakaninsu tare da yin alkawarin kawo karshen masu satar gangar man fetur da hare-haren da ake kai wa bututun man fetur da iskar gas a Nijeriya.
NNPC din da sojin ruwan, sun cimma wannan matsayar ne a yayin da Babban Daraktan ma’aikatar, Malam Mele Kyari ya kai wa shugaban hafsan sojojin Vice Admiral Ibok Ekwe-Ibas ruwan ziyara a hedikwatarsu dake birnin tarayya Abuja a ranar Laraba.
A wani sanarwa da Kakakin NNPC din ya fitar, Ndu Ughamadu ya ce Kyari ya nuna jindadinsa bisa wannan hadakar da suka yi da sojin ruwan domin ganin an tsare man fetur din Nijeriya da iskar gas daga bata gari da barayin ruwa.