Wani dattijo mai shekaru 57 ya lissafo sharuddan da yake nema wurin matar aure ta biyu da yake nema wanda lamarin ya bazu a kafafen sada zumuntar zamani, intel region.com ta ruwaito.
Wata kafa ta hada auratayya ta yanar gizo da ke Twitter ta bayyana cewa mutumin ma’aikacin gwamnati ne kuma yana da digirin digir, kuma genotype dinsa AA ne sannan rukunin jininsa O+ ne.
KU KARANTA: Muna da mata 44m, maza 49m da suka yi rijistar katin zaɓe, INEC
Yana neman matar aure ta biyu kuma tsaka-tsaki yake so, ba mai kiba ba kuma ba siririya ba, sannan shekarunta su kasance tsakanin 25 zuwa 35.
Yana son mai addini, natsuwa da tsoron Allah. Ya ce zai so ace ta kasance mahaddaciyar Al’Qur’ani.
Ya kuma bayyana cewa zai biya sadakin N500,000 zuwa sama, amma ba sai ta zo da kayan daki ba kuma ba za a yi wani shagali ba a auren.
Nan da nan kafar ta bukaci matan da ke suka cika sharuddan da su tura sako na kai tsaye don a duba su. Ya kuma ce ba zai yi lefe ba.
Cikin Mintuna 5, ‘Yan Damfara Suka Talauta Mahaifiyata Bayan Wawure N381.6m Daga Asusunta, Matashi Ya Koka
A cewar mutumin da ya ba da labarin a dandalin sada zumunta na Reddit, ‘yan damfara sun shafe mintuna biyar suna waya da mahaifiyarsa kafin su aikata mata na bera.
Ya bayyana cewa sun shawo kan babbar matar ta shiga cikin yanar gizo na bogi inda ta shigar da bayanan asusunta.
Mutum ya ba da labarin yadda masu satar cryptocurrency suka shawo kan mahaifiyarsa ta bada bayanan shiga zuwa asusunta na Coinbase.