Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari a ranar Juma’a a Addis Ababa Ƙasar Ethiopia, yace zai cigaba da jajircewa wajen cire talakawa da Marasa Ƙarfi daga ƙangin talauci har sai zuwa ƙarshen wa’adin mulkin sa a Shekarar 2023.
Shugaban Ƙasar ya bada wannan tabbacin a lokacin da yake jawabi a taron gabatar da rahoto na Ƙungiyar Ƙasashen Afirka, inji Wata sanarwa da mai magana da Yawun Shugaban Ƙasar Femi Adesina ya fitar.
KARANTA WANNAN LABARIN: ‘Yan Sandan Amurka Sun Wallafa Faifan Bidiyon Da Yake Nuna Yadda Wani Jami’i Ya Harbe Bakar Fata
Buhari Yayi nuni dacewar kula da cewa za’a hana talauci shigowa, a yayinda za’a baiwa ilmi fifiko domin samun sa yanda ya kamata.
Yasha alwashin cewa gwamnatin sa zata yi amfani da batun ICT domin ɓullo da ayyukan yi.
Shugaban ya jaddada cewa tana cigaba da ƙwazo kuma zata cigaba da zama mamba na Ƙungiyar Afirka ta Peer Review Family.