Mai Martaba Sarkin Zazzau Ambasada Nuhu Bamalli yasha Alwashin cigaba da bada goyon baya ga Hukumar kula da Shige Fice ta Najeriya reshen Jihar Kaduna, domin ganin an magance ƴan ta’adda da sauran waɗanda ke shigowa Jihar domin aikata ta’addanci.
Sarkin ya bayyana hakan a jiya ranar laraba a Lokacin da Sabon Kwanturolan Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa reshen Jihar Kaduna, Malam Liman Sani Kila, ya kai mashi ziyarar ban girma a fadarsa da ke birnin Zariya.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yajin Aikin ASUU: Wata Daliba Ta Nemi Kotu Ta Hana Buhari Da Gwamnoni Albashi
Mai martaba sarkin Yasha alwashin bayarda da duk irin gudunmawar da hukumar ke bukata musamman a Kokarin ta na yaki da masu Aika muggan laifuka ta hanyar kutse ba bisa ka’ida ba.
Sani liman kila Wanda ya samu ƙarin Girma Babu jumawa zuwa matakin Kwanturola a hukamar ta kula da shige da fice, an nada shi Kwanturolan jihar Kaduna ne Jim ka’dan Bayan samun Karin Girman.
kafin a Naɗin sa, Sani Kila shine Mai kula da ofishin fasfo na Jihar Kano.
Sani kila ya kasance mutumen da akayi shaidarsa da aiki tukuru da tsayuwa Kan magana daya tare da tsayar da Gaskiya da Riko Amana a aikinsa.
A jawabin sa, Sani Kila ya bayyana ire iren Ayyukan da hukumar ke gudanarwa ga sarkin Zazzau da kuma goyon baya domin ganin an samu nasara.
A wani labarin kuma: Osinbajo Na Son Karin Mata Masu Matsayi A Shugabanci
Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya ce samun daidaito da adalci, wakilcin mata da shiga harkokin siyasa da gwamnati zai yi babban tasiri ga makomar zamantakewar tattalin arzikin kasa da kuma ci gaban kasa baki daya kamar misalin ilimin ‘ya mace.
Farfesa Osinbajo ya bayyana haka ranar Alhamis a matsayin babban bako na musamman a taron shugabanni mata na 2022.