Gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike ya ce zai bayyanawa mutanen Rivers wadanda za su kada wa kuri’a a zaben 2023 mai zuwa.
Wike ya ce a matsayinsa na gwamna, ya san dukkannin ‘yan takarar da zasu fafata a zaben mai zuwa.
Ya ce yana matukar kaunar jihar Rivers don haka ba zai bari jama’a su yi kuskure wajen zaben shugabannin su a 2023 ba.
Wike na wannan jawabi ne a wajen kaddamar da ginin Waterlines da aka gyara a Fatakwal babban birnin jihar a yau Laraba.
Ya kara da cewa, “za mu gaya muku wadanda za ku zaba, na san shi kuma zan gaya muku wanene shi.
“Yawancin ku ba ku sani ba, akwai masu son zuwa nan don kawai su zama gwamna ba tare da wani kuduri ba.
“Jihar Rivers ta yi mana abubuwa da yawa, don haka jihar ta na bin mu bashi da yawa” inji Wike
Gwamnan ya kuma caccaki wasu ‘ya’yan jam’iyyar PDP, wadanda ya yi gargadin cewa ba a cin zabe a otal-otal da ke Abuja, sai dai tun daga tushe.