Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a Jam’iyyar PDP yace idan aka zaɓe shi a matsayin Shugaban Ƙasa na Najeriya, zai yi aiki tuƙuru da Ƴan Majalisu domin sake fasalin Najeriya.
Abubakar ya bayyana haka a ranar Asabar a Calabar a lokacin da yake jawabi da Wakilan Jam’iyyar da masu ruwa da tsaki, a yayinda Jam’iyyar ta shirya gudanar da zaɓen fidda Gwani a ranakun 28 da 29 na wata Mayu.
Tsohon shugaban kasar yace zai bada gashin kai ga Jahohi da Ƙananan Hukumomi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ku Mutunta Sarkin Musulmi — MURIC ga Masu Zanga-zanga a Sokoto
A cewar sa, za’a samu matsala idan har ba’a zaɓi nagartattun mutane a Shekarar 2023.
“Tarihi zai maimaita kanshi idan har masu kaɗa ƙuri’a basu zaɓi mutanen daya kamata su zaɓa domin su jagorance su.
“A shirye nake, na cancanta, ina dukkanin abinda ake buƙata, wanda shiyasa na bada kaina domin in Jagoranci Ƙasar.
“Ina da jajircewa na kawo gyara matsalar tsaro,” yana mai ƙara dacewa, Jam’iyyar PDP bazata taɓa amincewa ta kasance abokiyar hamayya ba.
Shima da yake jawabi a taron, Mr Liyel Imoke Tsohon Gwamnan Jahar Cross River, ya yabawa Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasar da irin namijin ƙoƙarin sa, yana mai cewa ya kasance waɗanda suka yanke wa PDP cibiya.
Imoke yace Atiku Abubakar shine wanda mutane suka zaɓa a Shekarar 2019 duk da bashi yaci zaɓe ba.
Yace PDP a Jahar Cross River ta Kasance iyali ɗaya, kuma zasu bada goyon baya a gareshi.
Idan dai za’a iya tunawa, Atiku Abubakar ya nemi Gwamnan Adamawa a Shekarar 1990 da 1997 zuwa 1998 kamin ya zama Abokin Takarar Tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo a Shekarar 1999.