Atiku Bunkudu gwamnan jihar Kebbi, yace shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya umarci gwamnonin Arewa maso Gabas da su kawo karshen ta’addanci dake addabar yankin su.Kamar yadda Jaridar the cable ta wallafa a shafinta
Kamar yadda hukumar watsa labarai ta kasa ta ruwaito, Bungudu ya bayyana haka ne a wajan taron shawo kan matsalar tsaro da bunkasa hadin kai tsakanin Fulani da ya gudana a Birnin Kebbi.
Gwamnan yace, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada wannan umarnin ne don gaggauta wanzar da zaman Lafiya a yankin.
KARANTA:- Wata sabuwa: Haryanzu Kamfanin Airtel bai sabunta Lasisin shi ba, inji NCC
Ya cigaba da cewa shugaban Kasa Muhammadu Buhari na iya bakin kokarin sa wajan kare rayukan Yan kasa kamar yadda tsari ya tanadar.
Gwamna Bungudu ya kuma yabawa sojoji da sauran Jami’an tsaro kan yaki da ta’addanci da sukeyi a wannan kasar.
Abunda ya shafi matsalar tsaro abu ne da ya shafi kowa, dole mu hada hannu don kawo karshen ta’addanci nan. Bungudu
Gwamna Bungudu yace a shirye yace wajan Jagorantar jami’an tsaro wajan kubutar da yaran makarantar sakandire ta Yawuri Jahar Kebbin.
Idan baku manta ba a watan July Sha bakwai ne suka kwashe Daliban makarantar.
Kawo yanzu dai jami’an tsaro sunce sun sami damar kubutar da mutane sha daya daga cikin wadanda aka sace.
Gwamnan yace ba wai an zabe mu bane kawai mu dinga zama a ofishi, hakkin mune kare lafiyar duk dan kasa na gari.
Zamuyi duk abunda ya kamata wajan samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali, idan ta kama mu sadaukar da kanmu ne zamuyi hakan, kamar yadda addini ya tanada.