‘Yar takarar gwamnan jihar Kogi a jam’iyyar SDP, Natasha Akpoti, a zaben da zai gudana a ranar 16 ga watan Nuwamban shekararnan, ta yi alkawarin kawo karshen nuna wariya da ake nuna wa mata a siyasar Nijeriya idan har ta samu nasarar lashe zaben gwamnan da za a yi.
Akpoti ta yi wannna alkawarin ne a yayin da take ganawa da mata a birnin tarayya Abuja a yayin da take neman goyon bayansu kan takarar da take yi. Kungiyar mata ta kasa wato NCWS ce ta shirya taron domin nuna goyon bayansu ga ‘yar takarar .
Ta kara da cewa; mata a matsayin ni iyayen kowa suna fuskantar kalubale, kuma ana nuna musu wariya musamman a cikin gwamnati da kuma siyasar kasarnan. Sannan ta nuna takaicinta bisa yadda aka jefa jihar cikin mawuyacin hali. Sannan ta ce dole ne a kalli mata a matsayin wadanda za su iya jagorantar shugabanci na gari da kawo ci gaba a jihar.