Zan taya murna ga Kowacce Jam’iyya taci zaɓen Shugaban Ƙasa a 2023 — Hadimar Buhari
Mai Taimakawa Shugaban Ƙasa Muhammadu akan Kafafen Sadarwa na Zamani Ms Lauretta Onochie a ranar Alhamis bata matsalar da batun tsarin karɓa-karba na Shekarar 2023, inda har suka fito da Jajirtaccen Shugaba.
KARANTA WANNAN LABARIN: Mutumen da yayi Safarar Matar shi don Karuwanci, ya saida Ɗan sa N600,000
A cewar ta zata taya murna ga dukkan wanda ya lashe zaben daga Jam’iyyar APC, ko kuma Jam’iyyar PDP.
“Duk wanda yaci zaɓe daga APC ko PDP, zan tashi murna akan nasarar da yayi.
“Ban damu da inda Shugaban Ƙasa zai fito ba, indai har ya kasance mutum ne dake son Ƙasar, kamar yadda nake yi,” inji ta.
Hadimar an dai ƙi tantance ta matsayin Kwamishinar Tarayya daga jerin sunayen da Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya tura domin naɗa su a Hukumar Zaɓe mai Zaman Kanta, inda aka musanya ta da Mrs May Agbamuche Mbu Sakamakon ƙorafi daga ƴan Najeriya.
Inda Majalisar Dattijai ta ƙi amincewa domin naɗa ta.
Comments 1