A ci gaba da yaƙi da annobar Korona da gwamnatocin ƙasar nan ke yi, a ranar Laraba gwamna Darius Ishaku na jihar Taraba, ya ce gwamnatinsa tana ci gaba da faɗi-tashin ganin ba a samu wanda cutar Korona za ta kashe ba a jiharsa.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin da mambobin kwamitin yaƙi da cutar Korona na jihar ƙarƙashin jagorancin shugabanta, Dokta Innocent Vakkai, suka gabatar da cikakken bayanin ayyukansu a fadar gwamnatin da ke Jalingo.
Ya ce gwamnatinsa a halin yanzu tana faɗaɗa cibiyar gwaji da wuraren killace masu ɗauke da ƙwayoyin cutar domin tabbatar da an bayar kulawa ta musamman wajen yaƙi da cutar a jihar.
Gwamnan ya kuma shaidawa kwamitin cewa gwagwarmayar da gwamnatinsa take yi wajen yaƙi da cutar ya sanya aka samu ƙarancin mutanen da suka kamu da ita kuma babu wanda ta kashe har kawo yanzu.
Ya yi kira ga al’ummar jihar da su ci gaba da yi wa dokokin da muhukuntan lafiya suka shar’anta biyayya don daƙile yaɗuwar cutar.
Sai dai saɓanin yadda gwamnan ya bayyana, alƙaluman jukumar daƙile yaɗuwar cututtuka ta ƙasa (NCDC) sun nuna cewa, cutar Korona ta hallaka mutum 6 a Jihar Taraba yayin da kuma mutane 95 suka kamu da cutar.