Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya ce zai yi iya bakin ƙoƙarinsa wajen ganin an dai daita farashin kayyakin masarufi da suka yi tashin gwarzaon zabi a faɗin ƙasar nan.
Buhari ya bayyana hakan ne a shafinsa na Twitter kan halin matsin rayuwa da al’ummar ƙasar nan suka tsinci kansu a ciki dangane da tashin kayyakin masarufi.
Shugaba Buhari ya ce tashin kayayyakin masarufin ya biyo bayan ɓullar cutar Korona ne da kuma ambaliyar ruwa da matsin tatalin ariziƙi da ƙasar nan ta samu kanta a ciki.
A halin da ake ciki yanzu mutane na tofa albarkacin bakinsu dangane da irin halin matsi da aka tsinci kai a ciki, wasu na ganin shugaba Buhari bai taɓuka komai ba face koma baya da kuma saka rayuwar talaka cikin matsanancin hali.