Mista Godwin Obaseki na jihar Edo ya tabbatar da cewa yana nan daram a Jam’iyyar APC babu inda zai je duk dai ana yi masa makarkashiya wajen ganin ya fadi a zabe mai zuwa.
Obaseki ya bayyana hakan ne a jiya a Abuja inda yace duk rintsi duk wuya yana nan a APC babu inda zai je.
Obaseki yana fuskantar kalubale daga wani yanki na Jam’iyyar APC na jihar wanda su magoya bayan tsohon gwamnan jihar Adams Oshiomhole, wanda su sun fi so tsohon sakataren gwamnatin jihar Fasto Osagie Ize-Iyamu, da yayi sheka daga Jam’iyyar PDP zuwa APC da yayi takara a inuwar Jam’iyyar.
https://dimokuradiyya.com.ng/fadan-cikin-gida-kotu-ta-hana-obaseki-kama-oshiomhole/
Duk a cikin wannan tada hazo da ake yi ne, shugabanin Jam’iyyar jihar suka gana da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Bola Ahmed Tinubu domin ya shiga lamarin don ganin an kawo karshen rigimar bangaren guda biyu.
A yayin da wasu magoya bayansa suka kai masa ziyara a Lokoja, Obaseki ya bayyana cewa ba daidai bane a bawa wanda bashi da wani aikin mu zo mu gani tikitin takarar jihar.
“Na zabi na ci gaba da zama a Jam’iyyar APC wanda tun asali a cikinta na sami nasarar zama gwamna, kuma ba zan fita ba komai wuyar da zan fuskanta”. Cewar Obaseki.