Kwamishinan ‘yan sandan jihar Inugu, Ahmad Abdurrahman ya gargadi iyaye da ‘yan’uwa da abokan arziki da su daina barin ana amfani da ‘ya’yansu wajen haifar da matsalar tsaro a jihar.
Wannan gargadin ya fito ne cikin sanarwa da Kakakin rundunar ‘yan sandan shiyyar SP Ebere Amaraizu, suka fitar a ranar Juma’a a Inugu.
Sanarwar ta ce; sun samu bayanan sirri dake nuna cewa wadansu matasa a karkashin wata kungiya mai suna ‘Enugu North Youth’ sun shirya gudanar da zanga-zanga a jihar.
A cewar sanarwar zanga-zangar da wannan kungiya za su yi zai gudana ne a yau Asabar 28 ga watan Satumba a cikin Nsukka. Ya ce da wannan yake kira ga iyaye da ka da su yarda a rika amfani da ‘ya’yansu wajen haifar da matsalar tsaro a jihar.