Kungiyar dalibai ta kasa (NANS) ta yi kira da a gaggauta warware yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ta ke yi.
Kamfanin dillacin labarai na kasa NAN ya rawaito cewa, Zababben shugaban kungiyar NANS Umar Faruq-Lawal ne ya yi wannan kiran a Abuja yayin da yake jawabi ga manema labarai kan ci gaban yajin aikin na ASUU.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Faruq-Lawal ya yi kira ga ASUU da ta koma kan teburin tattaunawa tare da bude jami’o’in gwamnati a fadin kasar nan.
Ya kuma bayyana cewa kungiyar za ta yi zanga-zangar nuna rashin amincewa da yajin aikin da aka kwashe watanni kusa 8 ana yi, yana mai cewa matsalar ta jawo wa dalibai da iyaye da kuma tattalin arzikin ‘yan Najeriya shiga wahalhalun da ba a taba gani ba.
Shugaban ya kuma ce ya gabatar da gwagwarmayar ‘Academic Reforms’ ne domin karrama daya daga cikin mamban kungiyar NANS da ya rasu domin samar da jawabai kan ci gaban ilimi a kasar nan.
Karanta kuma: Kungiyar Dalibai Ta Kasa Ta Mayar Da Martani Ga Kalaman Minista
“Abin da kawai zan ce shi ne ASUU da Gwamnatin Tarayya su koma kan teburin tattaunawa su warware dukkan matsalolin cikin ruwan sanyi sannan su sake bude makarantunmu.
“Ba dalibai ne ke biyan albashin malaman ba, gwamnatin tarayya ce don haka ba mu da karfin baiwa gwamnati shawara ko malaman mu, kawai za mu iya cewa su biyun su koma kan teburin tattaunawa,” inji shi.
A halin da ake ciki, Shugaban Majalisa na NANS, Adediwura Adeshina, ya ce shugabannin daliban za su yi taro domin yanke shawara kan ranar da za a gudanar da zanga-zanga.
“A cikin sa’o’i 24 masu zuwa, Shugaban NANS zai gana da zababben shugaban SUG na dukkan cibiyoyin.
” Kuma za mu yanke hukunci kan ranar da za mu mamaye ma’aikatar ilimi ta tarayya.
“Ba za mu tafi da ‘yan baranda ba amma daliban da ke da katin shaida,” in ji shi. (NAN)
A wani labarin kuma: Cibiyar NMC Ta Horar Da Malaman Lissafi 300 A Jihohi Guda Uku – Darakta
Farfesa Promise Mebine, Babban Darakta na Cibiyar Lissafi ta Kasa (NMC), ya ce cibiyar ta horar da malaman lissafi kusan 300 a cikin shekara guda da ya yi a kan karagar mulki.
Mebine ya bayyana hakan ne a cikin wata takarda da aka ajkewa Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa ranar Alhamis din nan a Abuja.