Wasu mutane a yankin Kudu maso Yammacin kasar nan, sun fito zanga-zangar kinjinin Ayyukan jami’an tsaron Amotekun, bayan zarkin kungiyar da kashe wani matashin saurayin a garin Ibadan dake jihar Oyo.
Rahotannin da Jaridar Dimokuradiyya ke samu na nuna cewa, ana gudanar da zanga-zangar ne a kan hanyar Agodi dake babban birnin jihar a yau Laraba, 18 ga watan Ogustan shekarar 2021.
KARANTA WANNAN LABARIN: APC ta sanar da ranar da za ta yi Gangamin ta
Fusatattun Matasan sun fito ne, domin nuna bacin ransu, kan kashe wani matashin dan shekara 15 da ake zargin jami’an kungiyar Amotekun din ne, da alhakin kisan.
Sai dai har kawo wa lokacin hada wannan rahoto, ba musami cikakken labarin yanayin da yankin da aka yi kisan ke ciki ba, kuma rundunar yan sandan jihar ba ta yi wani bayani a hukumance ba.