A ranar Talatar nan al’amuran kasuwanci sun durkushe yayin da wasu fusatattun mazauna jihar Ogun, suka fito domin nuna rashin amincewarsu da karancin sabbin kudin naira N200, N500, da N1000.
An gudanar da zanga-zangar ne a Sango-Ota, dake karamar hukumar Ado-Odo/Ota a jihar Ogun.
KU KARANTA: Wasu Kungiyoyi Sun Kaɗa Kuri’ar Goyon Baya Ga Buhari Da Emefele
Mazauna garin da suka je bankuna domin cire kudi sun ce ba za su iya samun kudadensu ba.
An ce sun fi tayar da hankali ne a lokacin da bankunan kasuwanci suka ki karbar tsoffin takardun naira domin ajiya.
A ranar Talata, masu zanga-zangar sun tare mahadar Joju na hanyar Idiroko zuwa Ota, lamarin da ya haifar da cikas.
A yayin da aka yi ta harbe-harbe a kan hanyar, jama’a sun yi wa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari kaca-kaca, inda suka zargi jam’iyyar APC da sanya talakawa cikin wahala.
A halin da ake ciki, an tattara ‘yan sanda domin su tsare bankuna da ma’aikatansu a Sango-Ota.
Idan zaku iya tunawa wata mummunar zanga-zanga ta afku a Abeokuta a makon da ya gabata, inda aka kaiwa bankuna hari aka harbe mutum daya. Kamar yadda jaridar Daily Post ta ruwaito.
A wani labarin kuma: Kano: Da Yawan Yan Kasuwa Da Masu Shaguna Sun Bujirewa Karbar Tsohon Kudi
Al’umma yanzu haka sun shiga cikin cikin wani hali na rashin tabbas, sakamakon yadda babban bankin kasa CBN ya dage cewa babu batun karin wa’adi.
Masu karbar tsofaffin kudi hakan ya sanya suka dakatar da karba, yayin da kuma a gefe guda suka shiga farautar sabbin, duk da karancin da suke yi wajen samu.