Rundunar Yan Sandar Najeriya ta musanta zargin cewa jami’an ta ne suka hallaka wata matashiya a yayin zanga-zangar rajin kafa kasar Yarbawa.
Wata sanarwa da kakakin rundunar Olumuyiwa Adejobi ya fitar, ta ce an kirkiro da wannan labari ne kurum da aniyar kawo rudani ko kum sanya fargaba a zukatan yan jihar Legas sa kasa baki daya.
Sanarwar “Yan sanda ba su harba alburushi mai rai ko kwalli daya ba”
“Wannan gawar da aka samu an sameta ne a kudundune, da tazara mai nisa ma da matattarar zanga-zangar, kuma jininta ma ya riga da ya bushe, alama ce ta cewa gawar ta daɗe”
Ko da yake babu wata alama ta harbe-harbe daga kowa bayan yan sandar, to amma sun musanta cewa sune suka hallaka ta.