Zanga-zangar adawa da sakamakon zaben ‘yan majalisar dokokin Iraki na baya-bayan nan ta rikide zuwa tashin hankali a Bagadaza, inda masu zanga-zangar suka yi tir da “magudi” da aka yi da jami’an tsaro kamar yadda suka zarga.
Magoya bayan kungiyoyin da ke goyon bayan Iran, wadanda suka yi rashin nasara mai yawa a rumfunan zabe, sun jefi jami’an tsaro da duwatsu, inda su kuma suka harba barkonon tsohuwa tare da harbin iska don tarwatsa jama’a a ranar Juma’a.
A wani lokaci ana jin karar harbe-harbe a wurin zanga-zangar, inda aka ce an kashe masu zanga-zangar biyu tare da jikkata wasu da dama daga bangarorin biyu.
Jaridar Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa har kawo yanzu Babu wani a hukumance da ya tabbatar da asarar rayuka a yayin tarzomar.
Sakamakon kuri’ar da ‘yan majalisar dokokin kasar suka kada a ranar 10 ga watan Oktoba ya nuna cewa, kungiyar da ke karkashin jagorancin jagoran mabiya Shi’a Moqtada al-Sadr ta samu kujeru 73. Wanda hakan zai sanya ta ci-gaba da rike matsayinta a matsayin kungiya mafi girma a majalisar dokokin Iraki.