Mahukunta kwallejin Fasaha (Polytechnic) ta Kauran Namoda da ke jihar Zamfara a ranar Juma’a sun bayar da umurnin rufe makarantar na tsawon makonni biyu bayan zanga-zangan da dalibai suka yi kamar yadda Daily Trust ta tabbatar.
Wasu daliban makarantar da aka gana da su sun bayyana cewa sun yi zanga-zangar ne saboda rashin tsaro, karancin ruwa da lantarki a makarantar. Sai dai a cewar sanarwar da makarantar da fitar mai dauke da sa hannun Hajia S. Abubakar a madadin shugaban makarantar ya ce dukkan daliban su fice daga makarantar kafin karfe 4.30 na yammacin ranar Juma’a 20 ga watan Satumba.
Hukumar makarantar ta ce ta dauki matakin ne sakamakon shawarwarin da jami’an tsaro suka ba su na cewa daliban su tafi hutun makonni biyu domin a magance kalubalan da suke fuskanta cikin wannan lokacin.
An gano shugaban makarantar, Alh. Salisu Abubakar Ciroma yana ta bai wa daliban hakuri inda ya ce hukumar makarantar za ta magance matsaolin cikin gaggawa kuma babu bukatar yin zanga-zangar tun farko. Ya ce zanga-zangar ta fara ne bayan wasu miyagu da ba a gano ko su wane ne ba sun kaiwa wasu daliban hari. Ya ce dalibai hudun da aka kai wa hari sun samu kulawa daga asibitin makarantar inda aka sallamo biyu a ranar da lamarin ya faru sannan sauran aka sallame su daga bisani.
Hukumar makarantar ta bukaci dukkan daliban su karbo wasikar alkawarin cewa ba za su sake yin zanga-zanga ba bisa ka’ida ba dauke da sa hannun iyayensu idan za su dawo daga hutun.